1 Agusta 2026 - 21:26
Source: ABNA24
Rahoto Cikin Hotuna | Na Tattakin Yaumul Arba'een – Rana Ta Uku A Kano Najeriya

Alhamdulillah, a ci gaba da tattakin Yaumul Arba'een na bana a yankin Kano da kewaye, wanda yan uwa musulmai Almajiran sheikh ibraheem zakzaky sukeyi a yau an yada zango a garin Kasuwar dogo, ƙaramar hukumar Bebeji, inda aka gudanar da hutun ɗan lokaci tare da sallah da kuma cin abinci ga mahalarta tattakin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Bayan kammala hutun, yan uwa husainawa sun ci gaba da tafiya cikin tsari da lumana zuwa masaukin kwana, yayin da masu hidima ke ci gaba da ba mahalarta abinci, ruwa da sauran abubuwan da suke buƙata domin sauƙaƙa musu tafiyar.

Muna roƙon Allah (SWT) Ya ba dukkan mahalarta lafiya da ƙarfin guiwa, Ya karɓi wannan ibada, Ya kuma ba su ikon isa inda suka nufa cikin aminci.

SK PRESS TV na ci gaba da kawo muku rahotanni kai tsaye daga tattakin Yaumul Arba'een. Ku ci gaba da kasancewa tare da mu domin samun sabbin bayanai.

Badaru Rabiu Mai Sufi  SK PRESS TV  1/8/2026

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha